Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAn fara shirye-shiryen jana’izar Ayatollah Ali Khamenei a Iran

An fara shirye-shiryen jana’izar Ayatollah Ali Khamenei a Iran

An fara shirye-shiryen jana’izar marigayi Jagoran Addini kuma Jagoran Koli na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, inda ake sa ran dubban mutane daga sassa daban-daban na ƙasar da kuma baƙi daga ƙasashe daban-daban za su halarci bikin bankwana da shi.

Ana sa ran manyan jami’an gwamnati, shugabannin addinai da wakilai daga ƙasashe da dama za su halarci jana’izar, yayin da hukumomin Iran suka tsaurara matakan tsaro tare da shirya wuraren karɓar masu zuwa.

Mutuwar Khamenei ta haifar da zaman makoki a faɗin ƙasar, yayin da al’umma ke ci gaba da bayyana alhini tare da gudanar da addu’o’i domin girmama gudummawar da ya bayar tsawon shekarun jagorancinsa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments