Shekara ɗaya kenan da rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwa kuma fitaccen mai taimakon al’umma, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, wanda ya rasu yana da shekaru 94 a duniya a ranar 28/06/2025.
Marigayin ya shahara wajen taimakon al’umma, tallafa wa harkokin ilimi, lafiya da addini, tare da bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban ƙasa. Rayuwarsa ta kasance abin koyi na karamci, tausayi da hidima ga jama’a.
Muna roƙon Allah (SWT) Ya gafarta masa, Ya yi masa rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa. Amin.
Shin da me al’umma ke tunawa da rayuwar marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata?