Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnati da jam’iyyar APC za su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Ya ce an ɗora wa duk masu riƙe da muƙaman siyasa alhakin ƙarfafa jam’iyya da wayar da kan al’umma, tare da tabbatar da cewa APC ta samu gagarumar nasara daga matakin shugaban ƙasa har zuwa ƙananan hukumomi.
Gwamnan ya kuma umarci duk masu muƙaman gwamnati da ba su yi rajista da APC ba da su gaggauta yin hakan.
A wani mataki na ƙarfafa gwiwar jami’an gwamnati, ya amince da rabon filaye ga sama da mataimaka 300, tare da ba kowannensu tallafin naira 100,000.
Shugabannin APC na Kano sun kuma bayyana cewa jam’iyyar ta fara shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027, suna masu cewa za su ci gaba da tallata ayyukan gwamnatin Tinubu da na gwamnatin jihar Kano.