Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiHisbah ta sanya ranar auren gata a Kano

Hisbah ta sanya ranar auren gata a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta shirya gudanar da daurin auren gata na angwaye 1,500 da amare 1,500 a ranar Juma’a, 3 ga Yuli, 2026, a Jihar Kano.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamandan Hisbah na Karamar Hukumar Birni kuma kakakin kwamandojin Hisbah na kananan hukumomi, Malam Hamidan Tanko Alasaka, ya fitar.

Sanarwar ta bayyana cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zai jagoranci taron, yayin da Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Imam Aminu Ibrahim Daurawa, zai wakilce shi a matsayin uban angwaye.

Haka kuma, Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, zai kasance uban amare.

Za a gudanar da daurin auren ne da misalin karfe 2:00 na rana a Babban Masallacin Juma’a na Kano, kuma an gayyaci daukacin al’ummar Musulmi da su halarta.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments