Rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta ce ta ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su a yankin Ogbido da ke Iyahmo, a Arewacin jihar. An sace mutanen ne yayin da suke aiki a gonakinsu.
Mai magana da yawun rundunar, Eno Ikoedem, ta ce bayan samun kiran gaggawa, jami’an ’yan sanda tare da hadin gwiwar masu sintiri da mafarauta suka bi sahun masu garkuwar zuwa cikin daji.
A yayin aikin ceton, jami’an tsaro sun yi musayar wuta da masu garkuwar, lamarin da ya tilasta musu tserewa tare da barin mutanen da suka sace. Dukkan mutanen 11, maza tara da mata biyu, an ceto su ba tare da sun samu raunuka ba.
Rundunar ta ce ta fara farautar waɗanda suka tsere domin cafke su da gurfanar da su a gaban kuliya.