Dakarun Rundunar Haɗin Gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA sun kashe wasu mutum biyu da ake zargin ‘yan ta’addan Lakurawa ne a wani samame da suka kai a yankin Sabarumawa da ke Jihar Kebbi.
A cewar rundunar, ‘yan ta’addan sun yi yunƙurin kai hari ne, amma dakarun suka yi musu kwanton ɓauna, inda suka kashe biyu daga cikinsu, yayin da sauran suka tsere da raunuka. Haka kuma, sojojin sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, alburusai da babur daga wurin da aka yi artabun.
Rundunar ta ce za ta ci gaba da gudanar da hare-hare domin murƙushe ‘yan ta’adda a yankin, tare da ƙarfafa al’umma su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai domin yaƙi da ta’addanci.