Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiGobara ta tashi a dakin karatun kiwon lafiya na jam’ar Usman Danfodiyo...

Gobara ta tashi a dakin karatun kiwon lafiya na jam’ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto

Wata gobara ta lalata wasu ofisoshi da na’urorin solar a Hamidu Ahmed Medical Library da ke Usmanu Danfodiyo University, Sokoto (UDUS), lamarin da ya haddasa asarar dukiyoyi.

Wata gobara ta lalata wasu ofisoshi da na’urorin solar a Hamidu Ahmed Medical Library da ke Usmanu Danfodiyo University, Sokoto (UDUS), lamarin da ya haddasa asarar dukiyoyi.  

Rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar Asabar, inda ta ƙone wani ginin da ke maƙwabtaka da ɗakin karatu da kuma na’urorin samar da wutar lantarki ta hasken rana. Sai dai an yi nasarar ceto littattafan ɗakin karatu da sauran muhimman kayayyaki ba tare da sun lalace ba.  

Hukumar jami’ar ta bayyana cewa an fara bincike domin gano musabbabin tashin gobarar, tare da ɗaukar matakan da suka dace don hana sake aukuwar irin wannan lamari a nan gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments