Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke wasu mutane bakwai da ake zargin manyan kwamandojin Boko Haram da ISWAP ne, yayin da suke dawowa Najeriya daga aikin Hajji ta filin jirgin saman Katsina.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan bayan Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan dokar NIMC Act 2026. Ya ce an samu nasarar cafke waɗanda ake zargin ne sakamakon haɗa bayanan Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC) da na Hukumar Shige da Fice da kuma sauran hukumomin tsaro.
A cewarsa, an kama mutanen ne a makon da ya gabata a Filin Jirgin Sama na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina, kafin daga bisani a miƙa su ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya, DSS domin ci gaba da bincike. Ya bayyana cewa sabon tsarin haɗa bayanan tantance mutane zai ƙara taimakawa wajen yaƙi da ta’addanci, satar bayanai da sauran laifukan tsaro a Najeriya.