Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaAtiku ya yi zargin ana ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasar jam’iyya ɗaya

Atiku ya yi zargin ana ƙoƙarin mayar da Najeriya ƙasar jam’iyya ɗaya

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya soki yunƙurin soke rajistar jam’iyyar NDC ta hanyar kotu, yana mai cewa hakan na nuna ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na karkata ƙasar zuwa tsarin jam’iyya ɗaya.

Atiku ya bayyana cewa bai yi mamakin wannan mataki ba, yana zargin cewa ana ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa domin bai wa Tinubu damar samun nasara a zaɓen 2027.

Ya jaddada cewa zaɓe mai ’yanci, gaskiya da adalci shi ne ginshiƙin dimokuraɗiyya, yana mai gargadin cewa duk wani yunƙurin tauye wannan hakki na iya jefa ƙasar cikin rikici da rashin zaman lafiya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments