Uwargidan Shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta jaddada cewa babu wani yaro da ya kamata ya kwanta da yunwa a fadin kasar nan.
Ta bayyana hakan ne yayin wata ganawa da matan gwamnoni, inda ta yi kira gare su da su kara kaimi wajen aiwatar da shirye-shiryen da za su rage yunwa da rashin abinci, musamman a tsakanin yara.
Oluremi Tinubu ta ce shirin Renewed Hope Initiative na ci gaba da mayar da hankali wajen inganta walwalar iyalai da tabbatar da wadataccen abinci ga al’ummomi masu bukata a sassan kasar.