Sunday, October 18, 2026
HomeIlimiJami’ar FUD ta fallasa  sunayen ma’aikatan da suka yi murabus bayan samun tallafin...

Jami’ar FUD ta fallasa  sunayen ma’aikatan da suka yi murabus bayan samun tallafin karatu daga Jami’ar

Jami’ar Tarayya da ke Dutse, FUD a Jihar Jigawa ta fitar da sunayen wasu ma’aikatanta da suka gaza komawa bakin aiki bayan kammala karatun da jami’ar ta ɗauki nauyin karatunsu.

Sanarwar, wadda magatakardar jami’ar Alhaji Abubakar Mijinyawa ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa ma’aikatan sun karya yarjejeniyar da suka kulla da jami’ar ta hanyar yin murabus ko kuma ƙin dawowa aiki bayan kammala karatu.

Daga cikin waɗanda abin ya shafa akwai Afolabi Lukman Olalekan na Sashen Kimiyyar Sinadarai da ake bin sama da Naira miliyan 12, Muhammad A. Alhassan na Sashen Kimiyyar Kwamfuta da ake bin sama da Naira miliyan 14, Yakubu Sani Wudil na Sashen Kimiyyar Lissafin Halittu da ake bin sama da Naira miliyan 18, da Ramla Muhammad Kama ta Sashen Magunguna da ake bin sama da Naira miliyan 16.

Jami’ar ta ce ta dakatar da albashin wasu daga cikinsu, ta aika musu da takardun bashin da ake binsu, sannan ta miƙa lamarinsu ga Kwamitin Ladabtar da Manyan Ma’aikata.

Ta kuma bayyana cewa wasu daga cikin ma’aikatan sun fara mayar da wani ɓangare na kuɗaɗen, yayin da ta gargaɗi duk masu karya yarjejeniyar cewa za ta ci gaba da ɗaukar matakan ladabtarwa tare da karɓo duk kuɗaɗen da ake binsu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments