Babbar Kotun Jihar Kano ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje da wasu mutum bakwai zuwa ranar 14 ga Oktoban 2026.
Ganduje, tare da matarsa Hafsat Umar Ganduje da sauran waɗanda ake tuhuma, na fuskantar tuhume-tuhume 11 da suka haɗa da cin hanci, haɗa baki, karkatar da kuɗaɗen gwamnati da kuma zargin wawure biliyoyin nairori na kuɗaɗen jama’a.
A zaman kotun da aka gudanar ranar Laraba, lauyan gwamnati ya bayyana cewa sun shirya ci gaba da shari’ar, inda ya nemi izinin kotu na janye wata buƙata da suka gabatar a baya domin maye gurbinta da sabuwar buƙata.
Lauyoyin Ganduje da wasu daga cikin sauran waɗanda ake tuhuma sun bayyana cewa ba su da wata adawa da wannan mataki.