Gwamnatin Jihar Kano ta rufe wani gidan shirya fina-finai da ke unguwar Bello a Dorayi, bayan zarginsa da karya dokokin tsara birane tare da gudanar da ayyukansa a yankin da aka tanada domin gidajen zama.
Matakin ya kasance ne karkashin shirin “Operation Show Your Document” na Hukumar Tsara Taswirar Filaye ta Jihar Kano (KANGIS), wanda Babban Daraktanta, Dalhatu Aliyu Sani, ke jagoranta.
Sani, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin yaki da gine-ginen da ba su da izini, ya bayyana cewa an dauki matakin ne sakamakon korafe-korafen da mazauna yankin da wasu malamai suka gabatar.
Ya ce binciken farko da hukumar ta gudanar ya nuna cewa gidan shirya fina-finan bai cika sharudda da ka’idojin doka da ake bukata ba, lamarin da ya sa aka rufe shi domin daukar matakan da suka dace.