Ƙungiyar Islamic Movement in Nigeria, IMN, wadda aka fi sani da kungiyar mabiya mazhabin Shi’a da ke ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibraheem Zakzaky, ta sanar da shirinta na gudanar da gangamin Ashura a ranar Juma’a, 26 ga Yuni, 2026, a matsayin wani ɓangare na tunawa da shahadar Imam Husain, jikan Annabi Muhammad (SAW).
A cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ce za a gudanar da gangamin a garuruwa da ƙauyuka sama da 600 da ke jihohi fiye da 23 da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja. Ta bayyana cewa an mayar da ranar gangamin zuwa Juma’a ne domin ya yi daidai da bikin tunawa da Ashura da ake gudanarwa a birnin Karbala na ƙasar Iraki.
Ƙungiyar ta ce Ashura na wakiltar tsayawa kan gaskiya, adalci da sadaukarwa, tana mai jaddada cewa gangamin na zaman lafiya ne kuma yana nuna biyayya ga Imam Husain da ƙin amincewa da zalunci a kowane lokaci.
Ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da gudanar da bukukuwan Ashura a Najeriya domin raya darussan Imam Husain na gaskiya, adalci da jajircewa wajen kare abin da ya dace.