Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta kama wasu buhuna 47 na kayan sojoji da kwalaye 80 na wasu kayayyakin da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne yayin wani samame da ta kai a yankin Surulere.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Fatai Tijani, ya ce an kama mutane uku da ake zargi da hannu a lamarin bayan jami’an sashen yaƙi da garkuwa da mutane sun gudanar da aiki bisa bayanan sirri a daren Asabar.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Chinedu David mai shekara 29, Ezeagwu Chukwuma mai shekara 38, da Ifeanyi Ogbeanyi mai shekara 45.
A cewarsa, an kama su ne tare da wata babbar mota mai amfani da dizal wadda ba ta da rajista, ɗauke da buhuna 47 na kayan sojoji da kuma kwalaye 80 na kayayyakin da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne.
Rundunar ta ce bincike kan lamarin na ci gaba domin gano tushen kayayyakin da kuma ko akwai wasu da ke da hannu a safarar su.