Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAdadin mutanen da cutar kwalara ta kashe ajihar Borno ya kai 108

Adadin mutanen da cutar kwalara ta kashe ajihar Borno ya kai 108

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a Jihar Borno ya ƙaru zuwa 108, yayin da adadin waɗanda ake zargin sun kamu da cutar ya haura 13,000.

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a Jihar Borno ya ƙaru zuwa 108, yayin da adadin waɗanda ake zargin sun kamu da cutar ya haura 13,000.

Rahotanni sun nuna cewa cutar ta bazu zuwa ƙananan hukumomi 19 na jihar, inda hukumomin lafiya ke ci gaba da ƙoƙarin dakile yaɗuwarta ta hanyar samar da cibiyoyin kula da marasa lafiya, tsaftace muhalli da wayar da kan al’umma.  

Hukumomin jihar sun ce suna aiki tare da ƙungiyoyin lafiya na cikin gida da na ƙasa da ƙasa domin shawo kan annobar, tare da ƙarfafa jama’a su riƙa amfani da tsaftataccen ruwa, kula da tsaftar muhalli da kuma garzayawa asibiti da zarar sun fara alamun cutar.  

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments