Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Kaduna ta gurfanar da mutane 24 a gaban kotun majistare bisa zargin hannu a kisan wata matar aure a Maraban Jos.
Ana tuhumar waɗanda ake zargin da laifukan haɗa baki wajen aikata laifi, tayar da hankalin jama’a, lalata dukiyoyi, da kuma kisan kai.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Yuni, 2026, lokacin da wasu fusatattun mutane suka ƙwace matar daga hannun jami’an tsaro kafin daga bisani ta rasa ranta.
Kotun ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 21 ga Yuli, 2026, tare da umartar a ci gaba da tsare dukkan waɗanda ake zargin har zuwa lokacin ci gaba da shari’a.
Haka kuma, rundunar ‘yan sanda ta ce bincike na ci gaba kan sama da mutane 100 da ake zargi da hannu a lamarin.