Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da kammala jigilar dawo da alhazan Najeriya daga Saudiyya bayan gudanar da aikin Hajjin 2026.
A cewar kakakinta, Hajiya Fatima Usara, jirgin ƙarshe mai ɗauke da alhazan Jihar Zamfara ne ake sa ran zai sauka a Najeriya, wanda hakan ke nuna ƙarshen aikin dawo da alhazan sama da 38,000.
Sai dai ta bayyana cewa har yanzu alhazai 12 na Najeriya suna karɓar magani a asibitocin Saudiyya, kuma hukumar na sa ido kan lafiyarsu tare da shirya dawo da su da zarar an sallame su.
NAHCON ta gode wa hukumomin jihohi, kamfanonin jiragen sama, jami’an lafiya, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudummawar da suka bayar wajen nasarar aikin Hajjin bana.