Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiAkalla manoma 18 sun rasa rayukansu a sabon harin da aka kai...

Akalla manoma 18 sun rasa rayukansu a sabon harin da aka kai a jihar Filato

Akalla manoma 18 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani sabon hari da wasu mahara suka kai ƙauyen Kawel da ke Gundumar Mushere, a Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato.

Akalla manoma 18 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon wani sabon hari da wasu mahara suka kai ƙauyen Kawel da ke Gundumar Mushere, a Ƙaramar Hukumar Bokkos ta Jihar Filato.

Shugaban matasan Bokkos, Christopher Luka, ya tabbatar da faruwar lamarin ga Daily Trust, inda ya ce harin ya auku ne da misalin ƙarfe 11:30 na daren Lahadi.

Rahotanni sun nuna cewa wannan hari ya zo ne ƙasa da kwanaki biyar bayan da aka kashe Hakimin Gundumar Gwande, Saf Samuel Alaket, a wani kwanton bauna da aka yi masa a hanyar Sha da ke kan iyakar al’ummar Daffo yayin da yake dawowa daga taron majalisar sarakuna.

Luka ya bayyana cewa wani shugaban matasa ne ya sanar da shi faruwar harin da tsakar dare, inda ya ce maharan sun buɗe wa manoma wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar sama da mutum 20, kafin daga bisani aka tabbatar da mutuwar mutum 18.

Ya ce, yana samu labarin, nan take ya sanar da jami’an tsaro da ke Bokkos, waɗanda suka tabbatar masa cewa sun riga sun samu rahoton harin kuma suna kan hanyarsu zuwa yankin.

Shugaban matasan ya bayyana harin a matsayin wanda aka kai ba tare da wani dalili ba, tare da yin kira ga jami’an tsaro su ɗauki matakan gaggawa domin dakile ci gaba da irin waɗannan hare-hare.

Har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Jihar Filato da Operation Enduring Peace ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments