Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroSojoji sun kuɓutar da matafiya 17 bayan harin ƴan ta’adda a Jihar...

Sojoji sun kuɓutar da matafiya 17 bayan harin ƴan ta’adda a Jihar Sokoto

Dakarun Sashe na 2 na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun yi nasarar ceto mutum 22 da aka yi garkuwa da su a wasu samame da suka kai a Ƙananan Hukumomin Sabon Birni da Isa na Jihar Sokoto.

A cewar mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanar Aliyu Danja, an gudanar da ayyukan ne bayan samun sahihan bayanan sirri da kuma kiran gaggawa daga al’ummomin yankunan.

Rahotanni sun nuna cewa a ranar 18 ga Yuni, 2026, wasu da ake zargin ƴan ta’adda ne sun tare hanyar Sabon Birni–Shinkafi a ƙauyen Kura Mota, inda suka kai hari kan motocin farar hula biyu tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama.

An kuma tabbatar da mutuwar wani farar hula yayin harin.

Bayan samun rahoton, dakarun sojin sun garzaya wurin tare da fara aikin ceto da bin sawun maharan, inda suka samu nasarar kuɓutar da mutane 22, ciki har da matafiya 17.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments