A cikin sanarwar da Fadar Shugaban Ƙasa ta fitar a ranar Asabar, Tinubu ya bayyana cewa rasuwar marigayiyar babban rashi ne ga iyalanta da kuma al’umma gaba ɗaya.
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aika saƙon ta’aziyya ga tsohon Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) kuma shugaban JIBWIS na Jihar Kano, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, bisa rasuwar matarsa, Hajiya Zainab.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ya yi mata rahama, Ya yafe mata kura-kuranta, tare da bai wa iyalanta da ‘yan uwa juriyar jure wannan babban jarrabawa.