Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroKebbi: ’Yan sanda sun cafke masu kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci

Kebbi: ’Yan sanda sun cafke masu kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci

Bayanan sirri sun taimaka wajen cafke waɗanda ake zargi da ta’addanci a Kebbi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi ta sanar da samun gagarumar nasara a yaƙin da take yi da masu aikata laifuffuka, inda ta kama mutane da ake zargi da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci da kuma ceto wata mata da aka yi garkuwa da ita.

Da yake jawabi ga manema labarai a Birnin Kebbi, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Umar Hadejia, ya bayyana cewa nasarorin sun samu ne sakamakon amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro, ƙungiyoyin sa-kai da kuma jami’an tsaro na CJTF.

A cewarsa, a ranar 5 ga Yunin 2026, jami’an ’yan sanda sun kama wasu mutane uku da ake zargi da kasancewa mambobin ƙungiyar Mamudawa/Boko Haram a kan hanyar Illo zuwa Lolo da ke ƙaramar hukumar Bagudo.

Waɗanda aka kama sun haɗa da Muhammadu Bandi, Aliyu Abubakar da Muhammadu Abubakar. Bincike ya nuna ana zargin suna kai wa ‘yan ta’addan da ke fakewa a yankin kayan abinci da sauran kayayyakin masarufi.

Kwamishinan ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna waɗanda ake zargin na yawan zirga-zirga a yankin Illo, kuma ana zargin suna da alaƙa da harin da ya yi sanadin mutuwar jami’an Hukumar Kare Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) uku a ranar 4 ga Yunin 2026.

Haka kuma, a ranar 7 ga Yunin 2026, rundunar ta sake kama wasu mutane huɗu da ake zargi mambobin ƙungiyar Lakurawa ne a kan hanyar Ka’oje zuwa Bakin Ruwa, cikin ƙaramar hukumar Bagudo.

Bugu da ƙari, jami’an ’yan sanda sun kama Murtala Sani, ɗan ƙauyen Zazzagawa da ke ƙaramar hukumar Argungu, bayan samun bayanan sirri da ke zarginsa da kai wa mambobin Lakurawa kayan abinci da abubuwan sha.

Ana kuma zargin Murtala Sani da jigilar wasu da ake zargi mambobin ƙungiyar zuwa maboyarsu a lokuta daban-daban.

Rundunar ta ce za ta ci gaba da ƙarfafa ayyukan tsaro a faɗin jihar tare da neman haɗin kan al’umma wajen bayar da sahihan bayanai domin daƙile ayyukan masu aikata laifuffuka.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments