Wani rahoto da kafar Axios ta wallafa ya ce Amurka da Iran sun rattaba hannu ta hanyar yanar gizo kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da ake sa ran za ta kawo ƙarshen rikicin da ya ɓarke a tsakaninsu tare da buɗe mashigar ruwa ta Hormuz.
A cewar rahoton, yarjejeniyar ta fara aiki nan take bayan shugabannin ƙasashen biyu sun kammala sanya hannunsu ta hanyar lantarki.
An bayyana cewa tun da farko an tsara gudanar da bikin sanya hannu kan yarjejeniyar a ƙasar Switzerland a ranar Juma’a, sai dai daga baya aka cimma matsaya cewa za a iya aiwatar da ita kafin wannan lokaci ta hanyar yanar gizo.
Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta kuma tabbatar da cewa bangarorin biyu sun amince shugabannin ƙasashensu su rattaba hannu kan yarjejeniyar ta hanyar lantarki domin gaggauta fara aiwatar da ita.