Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kakkausar barazanar mayar da martani mai tsanani kan Isra’ila, biyo bayan hare-haren da aka kai a kudancin Lebanon da suka yi sanadin mutuwar mutane hudu.
Rahotanni daga Al Jazeera sun bayyana cewa rikicin na ƙara ƙamari ne duk da wasu yarjejeniyoyi da aka ce an cimma tsakanin Tehran da Washington, da ake fatan za su taimaka wajen rage tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Rundunar sojin Iran ta Khatam al-Anbiya ta bayyana cewa idan Isra’ila ba ta dakatar da hare-hare a Lebanon ba, to za ta fuskanci martani mai tsanani daga Iran. Ta kuma zargi Isra’ila da karya yarjejeniyar tsagaita wuta sau da dama tun bayan kulla ta.
Sanarwar ta kuma jaddada cewa Iran ba za ta zuba ido ba yayin da ake ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula a Lebanon, tana mai gargadin cewa duk wani ci gaba da irin wadannan ayyuka zai haifar da martani mai tsauri.