Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, kuma mai takara a zaben bana, Peter Obi, ya ce idan aka zaɓe shi a 2027, zai shiga tattaunawa da ‘yan bindiga ko wasu masu ɗauke da makamai da ke nuna sha’awar zaman lafiya, domin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro a Najeriya.
Obi ya bayyana cewa manufarsa ita ce a samu zaman lafiya a ƙasar, kuma duk wanda ke da niyyar barin tashin hankali za a iya tattaunawa da shi domin a samu mafita.
Sai dai ya jaddada cewa gwamnati za ta yi aiki da matakan tsaro a kan duk wanda ke ci gaba da aikata laifuka ko ƙin bin doka.
Wannan furuci na sa ya sake jawo muhawara a fagen siyasa da tsaro, inda mutane ke bayyana ra’ayoyi mabambanta kan ko tattaunawa da ‘yan bindiga na iya zama mafita ko kuma haɗari ga ƙoƙarin yaki da ta’addanci.