Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiZulum ya ƙaddamar da gidaje 100 da sauran ayyukan raya ƙasa a...

Zulum ya ƙaddamar da gidaje 100 da sauran ayyukan raya ƙasa a Illela

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ƙaddamar da wasu manyan ayyukan raya ƙasa da Gwamnatin Jihar Sokoto ta aiwatar tare da haɗin gwiwar Shirin Raya Ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) a Ƙaramar Hukumar Illela.

Ayyukan da aka ƙaddamar sun haɗa da gidaje 100 da aka gina domin ’yan gudun hijira da waɗanda suka rasa matsugunansu sakamakon rikice-rikice, cibiyoyin zaman lafiya da sauyin yanayi, tashar samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana mai ƙarfin kilowatt 50, da kuma aza harsashin ginin Kasuwar Ƙasa da Ƙasa ta Illela.

An bayyana cewa ayyukan na da nufin inganta rayuwar al’umma, samar da ayyukan yi, ƙarfafa zaman lafiya da kuma bunƙasa tattalin arzikin yankin.

Sanarwar da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnatin Jihar Sokoto, Abubakar Bawa, ya fitar ta ce ayyukan na nuna irin muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da abokan hulɗar ci gaba wajen samar da abubuwan more rayuwa ga al’umma.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments