Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnati ta fara shari’ar sama da mutum 600 da ake zargi da...

Gwamnati ta fara shari’ar sama da mutum 600 da ake zargi da ta’addanci

Gwamnatin Tarayya ta fara ci gaba da shari’ar daruruwan mutanen da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci a kotunan Abuja.

Antoni Janar kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, ya ce gwamnati na da ƙudirin magance matsalar ta’addanci tare da tabbatar da an hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Ana gudanar da shari’un ne a kotuna daban-daban a lokaci guda, yayin da sama da mutum 600 ke fuskantar tuhume-tuhume masu alaƙa da ta’addanci. Wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma sun riga sun amsa laifinsu, inda kotu ta yanke wa mutum biyu hukuncin daurin shekaru 15 da 20.

Shari’un na gudana ne ƙarƙashin jagorancin manyan alkalan kotun tarayya da ke Abuja.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments