Wata sabuwar amarya mai suna Fatima na hannun jami’an tsaro bayan da ake zarginta da kashe mijinta, Auwalu, a unguwar Rimin Kebe da ke Jihar Kano.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Lahadi bayan wata takaddama da ta kaure tsakanin ma’auratan, wadanda aurensu bai kai wata biyu da kafuwa ba.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa mamacin ya samu munanan raunuka bayan da aka kai masa hari da wuƙa a gidansu. An ce ya fito yana neman taimako tare da bayyana cewa matarsa ce ta kai masa harin.
Wani mazaunin yankin ya ce an garzaya da Auwalu zuwa ofishin ’yan sanda kafin daga bisani a tura shi asibiti domin samun kulawa, amma ya rasu kafin a isa.
Rahotanni sun nuna cewa matar na zargin cewa an tilasta mata auren, lamarin da ake ganin ya haddasa sabanin da ya kai ga aukuwar lamarin.
Bayan faruwar al’amarin, jami’an ’yan sanda daga ofishin Zango da ke Ɗantamashe sun kama matar domin ci gaba da bincike.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ’yan sanda ta Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.