Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiDuk da kashe Naira biliyan 57.78 kan tsaro, matsalar rashin tsaro na...

Duk da kashe Naira biliyan 57.78 kan tsaro, matsalar rashin tsaro na ci gaba da tsananta a Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta kashe Naira biliyan 57.78 kan harkokin tsaro a watanni hudun farko na shekarar 2026, amma duk da haka matsalar rashin tsaro na ci gaba da tsananta a sassa daban-daban na Najeriya.

Wani rahoto ya nuna cewa duk da makudan kudaden da aka ware domin inganta tsaro, hare-haren ‘yan bindiga, sace-sacen mutane da sauran laifuffuka na ci gaba da jefa al’umma cikin fargaba.

Rahoton ya kara da cewa cikin kasa da mako guda, an samu aukuwar laifuffukan da suka shafi tsaro har guda 98 a fadin kasar, yayin da hare-hare da garkuwa da mutane suka kai 51, lamarin da ke nuna yadda kalubalen tsaro ke kara muni.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments