Yau, 16 ga watan Yuni, ya cika shekaru 13 da rasuwar Alhaja Abibatu Mogaji, mahaifiyar Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.
Alhaja Abibatu Mogaji ta rasu ne a ranar 16 ga Yunin 2013 a gidanta da ke Ikeja, Jihar Lagos, tana da shekaru 96 a duniya. An haife ta a ranar 16 ga Oktoban 1916 a birnin Lagos.
Marigayiyar ta shahara a fannin kasuwanci kuma ta taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin kasuwanci a Najeriya. Ta riƙe muƙamin Iyaloja ta ƙungiyar ‘yan kasuwa ta ƙasa bayan ta gaji fitacciyar shugabar kasuwa, Alimotu Pelewura.
Saboda gudummawar da ta bayar wajen ci gaban kasuwanci da tattalin arziki, gwamnatin tarayya ta karrama ta da lambobin yabo na ƙasa. Haka kuma, ta samu digirin girmamawa daga manyan jami’o’i da suka haɗa da Ahmadu Bello University da University of Lagos.
Alhaja Abibatu Mogaji ita ce mahaifiyar Shugaba Bola Tinubu da kuma kakar fitacciyar ‘yar siyasa, Folashade Tinubu-Ojo. Bayan rasuwarta, an yi jana’izarta a Ikoyi Vaults and Gardens da ke Jihar Lagos.
Har yau, ana ci gaba da tunawa da Alhaja Abibatu Mogaji a matsayin ɗaya daga cikin mata da suka taka rawar gani wajen bunƙasa kasuwanci da jagoranci a Najeriya.