Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya jaddada cewa mafita ga matsalolin da ke addabar yankin Arewacin Najeriya ba za ta samu ba sai an samu cikakken hadin kai tsakanin gwamnati, sarakunan gargajiya, malamai, hukumomin tsaro da kuma al’ummomi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron Sarakunan Arewa da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Jihar Jigawa da ke Dutse, inda manyan sarakuna da shugabanni daga jihohin Arewa 19 suka halarta.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, da kuma Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III.
A jawabin da ya gabatar, Namadi ya bayyana cewa yankin Arewa na fuskantar manyan kalubale da suka hada da rashin tsaro, talauci, rashin aikin yi ga matasa, rikice-rikicen manoma da makiyaya, shaye-shayen miyagun kwayoyi da kuma yawaitar yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ya ce wadannan matsaloli sun yi tasiri matuka wajen kawo koma baya ga ci gaban yankin, yana mai cewa babu wata hukuma ko bangare guda da zai iya magance su shi kadai.
Gwamnan ya yi kira ga sarakunan gargajiya da su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma, sasanta rikice-rikice da kuma karfafa zaman lafiya a tsakanin jama’a.
Ya kara da cewa sarakunan gargajiya na da kusanci da al’umma fiye da kowane bangare, lamarin da ke ba su damar taka rawar gani wajen magance matsalolin da ke addabar yankunansu.
Namadi ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa idan aka hada karfi da karfe tsakanin gwamnati, sarakuna, malamai da sauran masu ruwa da tsaki, za a samu nasarar magance kalubalen da ke hana yankin Arewa samun ci gaba mai dorewa.