Wata Babbar Kotun Tarayya a Najeriya ta umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) da ta soke rajistar wasu jam’iyyun siyasa guda biyar, bayan da kotun ta gano cewa sun kasa cika wasu sharuɗɗan da doka ta tanada.
Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa jam’iyyun ba su samu mafi ƙarancin kaso na ƙuri’un da kundin tsarin mulki ya tanada ba a babban zaɓen da ya gabata.
Jam’iyyun da hukuncin ya shafa sun haɗa da African Democratic Congress (ADC), Accord, Action Alliance (AA), Action Peoples Party (APP) da Zenith Labour Party (ZLP).
Kotun ta ce rashin cika waɗannan ka’idoji ya sa ya dace a soke rajistarsu kamar yadda dokar zaɓe da kundin tsarin mulki suka tanada.