Saturday, October 17, 2026
HomeWasanniIvory Coast ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta samu nasara...

Ivory Coast ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta samu nasara a Gasar Kofin Duniya ta 2026

Kungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Côte d’Ivoire ta kafa tarihi bayan ta zama ƙasar Afirka ta farko da ta samu nasara a gasar Kofin Duniya ta 2026. Elephants ɗin sun doke Ecuador da ci 1-0 a wasan farko na rukuni, inda suka fara gasar da ƙafa sama.

Sahararren dan wasan Manchester United Amad Diallo ne ya zura kwallon a mintuna na casa’in wanda hakan ya ba tawagar nasara. Wasan ya kasance mai zafi, inda ɓangarorin biyu suka samu damar zura ƙwallaye, amma tsaron Ivory Coast ya tsaya tsayin daka.

Kocin ƙungiyar, Emerse Fae, ya bayyana cewa tawagarsa ba ta je gasar domin yawon buɗe ido ba, sai dai domin yin tarihi da kai wa matakin gaba. Ya ce ‘yan wasansa sun nuna ƙwazo da jajircewa, kuma suna da burin tsallake zagayen rukuni a karon farko a tarihin ƙasar.

Nasarar ta ƙara wa magoya bayan Afirka kwarin gwiwa, musamman ganin cewa Ivory Coast ta dawo gasar Kofin Duniya bayan shafe shekaru 12 ba tare da halarta ba. Yanzu hankalin ƙungiyar ya koma kan wasanta na gaba da Jamus, wanda ake sa ran zai kasance babban ƙalubale.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments