Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiSojoji sun kama tsohon dan sanda da ake zargi da safarar makamai...

Sojoji sun kama tsohon dan sanda da ake zargi da safarar makamai a Filato

Dakarun Operation Enduring Peace sun cafke wani tsohon jami’in rundunar ‘yan sanda da ake zargi da hannu a safarar makamai a yankin Riyom da ke Jihar Filato.

A cewar rundunar, an kama mutumin ne a yankin Makera yayin da yake tafiya daga Karamar Hukumar Jos ta Kudu. Binciken da aka gudanar a cikin motarsa ya kai ga gano bindigogi kirar gida guda biyu, harsasai 167, barkonon tsohuwa da kuma wata wuka.

Haka kuma, jami’an sun kwato wayoyin hannu guda biyu, adduna biyu, katin shaidar aikin dan sanda, hotunansa cikin kayan aiki na ‘yan sanda, katunan ATM guda biyu, katin shaidar dan kasa da kuma Naira 73,300.

Rahotanni sun nuna cewa wanda ake zargin, Danjuma Yusuf, tsohon dan sanda ne da aka sallama daga aiki. Ana zarginsa da alaka da masu safarar makamai da kuma wasu kungiyoyin masu aikata laifuka da suka hada da masu garkuwa da mutane.

Rundunar ta tabbatar da cewa ana ci gaba da tsare shi domin zurfafa bincike da gano sauran wadanda ake zargin suna da hannu a wannan lamari.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments