Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai hari kauyen Pissa da ke karamar hukumar Borgu a Jihar Neja, inda suka kashe mutum uku tare da lalata gidaje da dama.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun mamaye kauyen ne da safiyar ranar, lamarin da ya haddasa firgici da tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar harin. Ya ce jami’an tsaro sun yi gaggawar kai dauki tare da tunkarar maharan, amma bai bayyana cikakken sakamakon artabun da aka yi da su ba.
Harin ya kara dagula halin tsaro a yankin, yayin da mazauna kauyukan da ke makwabtaka da wurin suka shiga fargabar yiwuwar sake kai wasu hare-hare.
A halin yanzu, hukumomin tsaro na ci gaba da gudanar da bincike tare da daukar matakan tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma a yankin.