Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana mutuwar tsohon jami’in soja, Major General Abubakar Rabe, a hannun masu garkuwa da mutane a matsayin abin kunya da kuma babban abin takaici ga tsaron kasa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Atiku ya ce rasuwar Janar Rabe na nuna yadda matsalar tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a Najeriya, duk da kokarin da ake yi na magance ta.
Ya ce abin takaici ne matuka jami’in da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare kasa da al’ummarta ya rasa ransa a hannun ‘yan ta’adda.
Atiku ya kuma danganta lamarin da sabon harin da aka kai a Chibok, inda aka kona makarantu da wasu kadarori, yana mai cewa hakan ya sake tayar da hankulan al’ummar da har yanzu ba su manta da mummunar sace daliban Chibok ba.
A cewarsa, hare-haren na nuna cewa ‘yan ta’adda na ci gaba da zama barazana ga rayuka, dukiyoyi da kuma bangaren ilimi a kasar.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa da masu tasiri wajen magance matsalar tsaro, yana mai cewa lokaci ya yi da za a wuce alkawura zuwa aiwatar da tsare-tsare da za su kare rayuka da dukiyoyin al’umma.