Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaRikici ya kunno kai a NDC bayan zargin miƙa wa INEC sunayen...

Rikici ya kunno kai a NDC bayan zargin miƙa wa INEC sunayen ‘yan takara

Rikici ya ɓarke a cikin jam’iyyar NDC bayan rahotanni sun nuna cewa shugaban kwamitin zaɓen fidda gwani na jihar Abia, Cif Asukewe Ikoawaji, ya aika da sunayen ‘yan takarar jam’iyyar kai tsaye zuwa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

An bayyana cewa sunayen da aka miƙa sun haɗa da na ɗan takarar gwamna, ‘yan takarar Majalisar Tarayya da kuma na Majalisar Dokokin Jiha daga jihar Abia.

Lamarin ya jawo ce-ce-ku-ce a cikin jam’iyyar, inda wasu mambobi suka yi zargin cewa an kauce wa tsarin da kundin jam’iyyar ya tanada wajen miƙa sunayen ‘yan takara ga INEC.

Wasu jiga-jigan NDC sun ce ikon tabbatarwa da miƙa sunayen waɗanda suka yi nasara a zaɓen fidda gwani yana hannun shugabancin jam’iyyar na ƙasa, musamman shugaban jam’iyya da sakataren ƙasa.

Takardun da suka fito sun nuna cewa Ikoawaji ya rubuta wa shugaban INEC wasiƙa ta hannun kwamishinan zaɓe na jihar Abia a ranar 30 ga Mayu, 2026, inda ya sanar da sakamakon zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 29 ga Mayu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments