Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiGwamnatin Sokoto ta ware Naira biliyan 1.65 don tallafa wa manoma

Gwamnatin Sokoto ta ware Naira biliyan 1.65 don tallafa wa manoma

Gwamnatin jihar Sokoto ta amince da kashe sama da Naira biliyan 1.65 domin sayen takin zamani, ingantattun iri da magungunan noma da za a raba wa manoma a daminar bana.

Hakan na kunshe ne cikin shawarwarin da Majalisar Zartarwar Jihar ta amince da su a taronta da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Sokoto, kamar yadda Darakta Janar na Yada Labarai da Hulɗa da Jama’a, Abubakar Bawa, ya bayyana.

Har ila yau, majalisar ta amince da sayen babura kirar Daylong guda 1,200 kan fiye da Naira biliyan 1.6, domin bai wa ma’aikatan gwamnati su ta hanyar tsarin rance.

Matakin na daga cikin alkawurran da Gwamna Ahmad Aliyu ya yi wa ma’aikatan jihar a lokacin bikin Ranar Ma’aikata.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments