Shugaban Amurka Donald Trump ya shiga wani yanayi na ɗan firgici a Fadar White House bayan wani tsuntsu ya ratsa sararin sama a lokacin da yake gabatar da jawabi.
Rahotanni sun bayyana cewa Trump ya dakatar da jawabinsa na ɗan lokaci, inda ya fara duba sama cikin alamar tsoro, yana tunanin ko jirgin mara matuƙi ne aka aika masa.
Shaidu sun ce shugaban ya yi saurin mayar da martani, yana cewa “Oh, oh,” kafin daga bisani ya bayyana cewa ya ɗauka kamar hari ne daga jirgin sama mara matuƙi.
Lamarin ya jawo dariya daga wajen ’yan jarida da ke wurin, yayin da ake ci gaba da rahotanni kan yadda tsaron sararin samaniyar Amurka ke ƙara zama mai tsauri a wannan lokaci.