Rundunar ‘yan sandan Kano ta sanar da kama mutane 345 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka haɗa da daba, safarar miyagun ƙwayoyi da kuma mallakar makamai masu haɗari a faɗin jihar.
Matakin ya zo ne yayin da ake ci gaba da samun rahotannin hare-haren ‘yan daba, tare hanyoyi da sace-sacen kayayyaki a wasu sassan jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan Kano, Ibrahim Bakori, ya bayyana cewa an samu nasarar kamen ne bayan wani samame na musamman da aka gudanar na kwanaki uku a ƙananan hukumomi 44 na jihar domin dakile ayyukan masu laifi da kuma ƙwace makamai da miyagun ƙwayoyi.