Wani sabon rikici ya dabaibaye jam’iyyar NDC bayan wasu manyan shugabanninta na shiyyar Arewa maso Yamma sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda suke zargin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da neman karɓe ikon tafiyar da jam’iyyar.
Shugabannin, ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban jam’iyyar na Arewa maso Yamma, Mohammed Serina, da shugaban jam’iyyar na Kano, Hussaini Mariga, sun bayyana damuwarsu ne cikin wata takardar korafi da suka miƙa wa jagoran jam’iyyar na ƙasa, Seriake Dickson.
A cewarsu, duk da irin tarbar da aka yi wa Kwankwaso bayan shigowarsa jam’iyyar da kuma damar da aka ba shi musamman a Kano, suna ganin yana ƙoƙarin karkatar da tsarin jam’iyyar zuwa tafiyar Kwankwasiyya kaɗai.
Sun kuma yi zargin cewa wasu mambobi da ba sa cikin tafiyarsa na fuskantar nuna wariya da kuma rashin samun damar shiga harkokin jam’iyyar yadda ya kamata.
Shugabannin sun yi kira ga shugabancin jam’iyyar na ƙasa da ya ɗauki matakin gaggawa domin tabbatar da adalci da haɗin kai, tare da kauce wa duk wani mataki da zai iya haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyyar.