Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kashe jami’an Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa (FRSC) guda uku a wani hari da suka kai a kan titin Tsamiya zuwa Illo da ke karamar hukumar Bagudo a jihar Kebbi.
Jami’an da suka rasa rayukansu sun hada da DCRMA Umar Aliyu, SRMA Ezra Manu Gona da kuma RMA I Mansur Ibrahim Nasir.
Rahotanni daga mazauna yankin sun nuna cewa jami’an na gudanar da aikinsu ne lokacin da maharan suka yi musu kwanton bauna tare da bude musu wuta.
Majiyoyi sun ce maharan sun kai sama da mutum 20, kuma bayan sun aikata harin sun tsere zuwa cikin daji ta hanyar amfani da babura.
Lamarin ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba yayin da ake kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa domin dakile irin wadannan hare-hare.