Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNSCDC sun dakile yunkurin sace mutane da kwashe shanu a Kano

NSCDC sun dakile yunkurin sace mutane da kwashe shanu a Kano

Jami’an hukumar NSCDC a jihar Kano sun yi nasarar dakile wani yunkurin sace mutane da kuma kwashe shanu da wasu mahara suka yi a yankin Bakin Komau da ke Dangora, karamar hukumar Kiru.

Mai magana da yawun hukumar, SC Ibrahim Abdullahi, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis lokacin da wasu ‘yan bindiga suka kai hari kan wani makiyayi, inda suka raunata shi tare da yin garkuwa da ‘ya’yansa biyu yayin kokarin sace dabbobinsa.

Bayan samun bayanan gaggawa, jami’an NSCDC da ke sintiri kusa da dajin Dansoshiya sun kai dauki cikin gaggawa, inda suka yi artabu da maharan.

A sakamakon hakan, maharan sun tsere cikin daji da raunukan harbin bindiga, tare da watsar da yaran da suka sace.

An ceto mutanen biyu da aka sace, Abubakar Saleh da Muhammad Inuwa Dille, kuma an mayar da su ga iyalansu cikin koshin lafiya.

Haka kuma, makiyayin da aka kai wa hari ya samu kulawar likitoci domin jinyar raunukan da ya samu.

Kwamandan NSCDC na Kano, Mohammed Hassan Agalama, ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da kira ga al’umma su rika bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments