Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn samu saukar farashin danyen mai a kasuwar duniya bayan gargadin da...

An samu saukar farashin danyen mai a kasuwar duniya bayan gargadin da Trump ya yi wa Natenyahu

Farashin danyen mai ya yi ƙasa da kusan dala uku kan kowace ganga a ranar Alhamis, bayan da masu zuba jari suka fara hasashen cewa rikicin da ya daɗe yana ci gaba a Gabas ta Tsakiya na iya samun sauƙi.

Saukar farashin ya zo ne a daidai lokacin da ake samun alamun tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Lebanon, lamarin da ya ƙara ƙarfafa fatan cewa za a samu kwanciyar hankali a yankin tare da yiwuwar sake buɗe mashigar Hormuz domin zirga-zirgar mai.

Rahotanni sun nuna cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin suka amince da ita ta taimaka wajen rage fargabar katsewar samar da mai a kasuwannin duniya.

Farashin ɗanyen mai na Brent ya sauka da dala 3.20, wanda ya kai kashi 3.27 cikin ɗari, inda ya tsaya a dala 94.61 kan kowace ganga.

Haka kuma, farashin mai samfurin US West Texas Intermediate (WTI) ya ragu da dala 3.71, ko kuma kashi 3.86 cikin ɗari, zuwa dala 92.31 kan kowace ganga.

Sai dai a ranar Laraba, farashin ya samu ƙarin kusan kashi 2 cikin ɗari sakamakon sabbin tashin hankula a yankin, ciki har da rahotannin hare-hare da kuma matsin lamba da ya shafi mashigar Hormuz.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments