Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn samu gagarumin ci gaba kan shirin kafa ‘yan sandan jihohi –...

An samu gagarumin ci gaba kan shirin kafa ‘yan sandan jihohi – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa shirin kafa ‘yan sandan jihohi zai taimaka matuƙa wajen ƙarfafa tsaro da kuma inganta tattara bayanan sirri a faɗin ƙasar nan.

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X.

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya ce an samu babban ci gaba a tattaunawar da ake yi kan samar da tsarin ‘yan sandan jihohi bayan wani taro da aka gudanar a Abuja.

A cewarsa, an fara nazarin batun ne watanni uku zuwa huɗu da suka gabata bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma yanzu an kai matakin duba sauye-sauyen da za a yi wa kundin tsarin mulkin ƙasa.

Gbajabiamila ya bayyana cewa kafa ‘yan sandan jihohi na buƙatar cikakken nazari saboda abubuwan da suka shafi dokoki da kundin tsarin mulki, yana mai cewa ba aiki ba ne da za a kammala cikin gaggawa.

Ya ƙara da cewa duk da ƙalubalen da ke tattare da shirin, gwamnati ta samu nasarori masu yawa a ƙoƙarin ganin an samar da tsarin da zai taimaka wajen magance matsalolin tsaro a Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments