Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiMa su ibadar da aka sace a cocin Kwara sun mutu a...

Ma su ibadar da aka sace a cocin Kwara sun mutu a hannun yan bindiga.

An tabbatar da rasuwar mutum biyar daga cikin masu ibada takwas da aka yi garkuwa da su yayin wani hari da aka kai cocin ECWA da ke Omugo, a yankin Oro Ago na karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara.

Faston cocin, Rabaran Timothy Omole, ya sanar da wannan mummunan labari ga mabiyansa ta wata sanarwa, inda ya bayyana cewa lamarin ya jefa shi cikin matsanancin jimami.

Daga cikin wadanda aka tabbatar da mutuwarsu akwai matar faston, Misis Rachael Oluwaremilekun Omole.

Sauran sun hada da Cif David Omopariola, Cif Joseph Ibitoye Afariogun, Misis Iyabo Aniyi da Dattijo Joshua Akanbi Adeyemi.

Rabaran Omole ya bayyana cewa daga cikin mutane takwas da aka sace a ranar 22 ga Maris, 2026, mutum uku ne kacal suka rage a hannun masu garkuwa da mutane.

A cewarsa, labarin mutuwar wadanda abin ya shafa ya fito ne daga wani daya cikin wadanda aka sace mai suna Sunday Bakare, wanda ya samu damar kubuta bayan shafe sama da wata guda a hannun masu garkuwa da mutanen.

Bakare ne ya dawo da bayanan abin da ya faru ga sauran wadanda aka tsare tare da shi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments