Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiTrump: Kwaso uranium daga Iran zai jefa Amurka cikin sabon rikici

Trump: Kwaso uranium daga Iran zai jefa Amurka cikin sabon rikici

Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa gwamnatinsa ba ta ga wata buƙata ta shiga Iran domin kwaso uranium ɗin da aka tace da ke ƙasar.

A wata hira da ya yi a daren Alhamis, Trump ya ce an binne uranium ɗin a wani wuri mai wahalar isa, wanda hakan ya sa duk wani yunƙurin kwaso shi zai kasance mai tsada da haɗari.

Ya ce tun farko an yi nazarin yiwuwar gudanar da irin wannan aiki, amma daga baya aka fahimci cewa zai buƙaci manyan kayan aiki da kuma ɗaukar lokaci mai tsawo a yankin da ake fama da rikici.

Trump ya jaddada cewa Iran ba kamar Venezuela ba ce, inda za a iya shiga a gudanar da aiki cikin sauƙi.

A cewarsa, aikin zai buƙaci jigilar manyan na’urori ta sama da kuma kasancewa a yankin yaƙi na tsawon mako guda ko fiye.

Shugaban na Amurka ya ƙara da cewa duk da cewa Amurka na da ƙarfin ɗaukar uranium ɗin idan ta ga dama, amma a halin yanzu babu wani dalili da zai sa ta ɗauki wannan mataki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments