Sunday, October 18, 2026
HomeLafiyaMutane sama da 4,000 sun kamu da cutar kwalara yayin da 39...

Mutane sama da 4,000 sun kamu da cutar kwalara yayin da 39 suka mutu a Borno

Akalla mutane 39 sun mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a jihar Borno, yayin da adadin wadanda ake zargin sun kamu da cutar ya haura 4,200 a wasu kananan hukumomin jihar.

Jami’an lafiya sun bayyana hakan ne a wani taron fadakarwa da aka gudanar a Maiduguri, inda aka tattauna hanyoyin kariya da kuma magance cutar zawo mai tsanani.

Shugaban Cibiyar Kula da Harkokin Gaggawa ta Lafiya ta Jihar Borno, Dakta Jacob Thlizer, ya ce an samu karin mutane 274 da ake zargin sun kamu da cutar cikin awanni 24 kacal.

A cewarsa, adadin wadanda ake zargi da kamuwa da kwalara ya kai mutum 4,204 a unguwanni 36 da ke cikin yankunan da annobar ta shafa, yayin da yawan wadanda suka rasa rayukansu ya kai 39.

Ya kara da cewa cutar ta bazu zuwa kananan hukumomi da dama da suka hada da Jere, Bama, Kaga, Mafa, Kwaya Kusar, MMC, Konduga, Monguno, Magumeri da Ngala.

Bayanan da aka tattara sun nuna cewa karamar hukumar MMC ce ta fi fama da cutar, inda aka samu mutane 2,404 da ake zargi sun kamu, sai Jere da mutum 1,214.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments