Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da ware Dala miliyan 3.5, kwatankwacin kusan Naira biliyan 5, domin tallafa wa inganta tattara bayanai da bayar da rahotanni kan take hakkin addini a Najeriya.
Shirin, wanda Ofishin Kula da ’Yancin Addini na Amurka ya kaddamar, yana neman kungiyoyi da za su taimaka wajen bibiya, tattara bayanai da bayar da rahotanni kan hare-haren da suka shafi addini da akida a sassan Najeriya.
A sanarwar da aka fitar ranar 22 ga Mayu, 2026, an bayyana cewa shirin zai gudana na tsawon shekara biyu zuwa hudu, inda ake sa ran kungiya daya za ta samu tallafin.
Gwamnatin Amurka ta ce manufar shirin ita ce kara karfin sa ido da rubuta bayanai kan take hakkin addini da wasu cin zarafi da jami’an gwamnati ko kungiyoyin da ba na gwamnati ba ke aikatawa, domin inganta daukar matakan ladabtarwa da wayar da kai.
Sanarwar ta yi nuni da hare-haren da kungiyoyin Boko Haram, ISWAP, makiyayan da ake zargi da aikata ta’asa da sauran kungiyoyin masu dauke da makamai ke kaiwa, tana mai cewa duka Kiristoci da Musulmi sun sha fama da irin wadannan hare-hare.
Haka kuma, Amurka ta yi zargin cewa hukumomin Najeriya ba sa mayar da martani cikin gaggawa ko yadda ya kamata ga hare-haren da ake kai wa al’ummomin addinai, lamarin da ta ce yana kara karfafa rashin hukunta masu laifi.
Sanarwar ta kuma yi ikirarin cewa akwai rahotanni masu inganci da ke nuna wasu jami’an tsaro sun taba kai samame wuraren ibada yayin neman wadanda ake zargi da aikata laifuka.
Shirin tallafin ya biyo bayan matakin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya dauka a watan Nuwamban 2025 na ayyana Najeriya a matsayin kasa mai matukar damuwa kan batun ’yancin addini.
Kungiyoyin da za su nemi tallafin ana sa ran za su mayar da hankali kan sa ido, tattara bayanai da bayar da rahotanni kan take hakkin addini, musamman a yankin Middle Belt, tare da bayyana akalla jihohi hudu da za su aiwatar da ayyukansu.
An bude damar neman tallafin ga kungiyoyin sa-kai na cikin gida da na kasashen waje, kungiyoyin kasa da kasa, jami’o’i da wasu kamfanoni masu zaman kansu. Za a rufe karbar bukatun neman tallafin ranar 9 ga Yulin 2026.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta sha musanta zarge-zargen gallazawa mutane saboda addininsu, tana mai cewa matsalar tsaro tana shafar ’yan kasa ba tare da la’akari da addininsu ba, tare da jaddada ci gaba da hadin gwiwa da Amurka wajen yaki da ta’addanci da inganta tsaro.