Wani limami a jihar Katsina na fuskantar zargi bayan rahotanni sun bayyana cewa ya aurar da wasu daga cikin ’yayansa ga junansu domin cin gajiyar shirin auren gata da ake gudanarwa a jihar.
Rahotannin sun nuna cewa ana zargin limamin da shirya auren ne ta hanyar hada wasu maza da mata da ke da alakar jini ko ta dangi domin su samu damar amfana da tallafin da ke tattare da shirin.
Lamarin ya janyo cece-kuce a tsakanin al’umma, inda wasu ke kira ga hukumomin da abin ya shafa da su gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar zargin tare da daukar matakin da ya dace idan an tabbatar da laifi.
Har zuwa yanzu, ba a samu wata sanarwa a hukumance daga bangaren limamin ko hukumomin da ke kula da shirin dangane da zargin ba.